Janyewar hukumar USAID na daɗa haifar da bazuwar cutar HIV a Bauchi

USAID USAID 750x430

Janyewar jukumar ba da Alagajin gaggawa ta Amurka (USAID) daga ayyukan rigakafin cutar kanjamau a jihar Bauchi ya kara kaimi wajen yaduwar cutar a jihar.

Abdulahi Ibrahim, shugaban kungiyar masu fama da cutar HIB a Najeriya (NEPWHAN), reshen Bauchi ne ya bayyana hakan, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda ake fama da karancin cibiyoyin jinya, da bada tallafi a asibiti.

Ya yi gargadin cewa rashin samun kulawa ga masu cutar na iya haifar da kalubale babba.

“Muna da masu aikin sa kai sama da 22,000 a jihar, wadanda da yawa a halin yanzu ba su da aikin yi kuma ba za su iya taimakawa wajen ba da kulawa ba,” in ji Ibrahim.

Ya bukaci gwamnatin jihar da ta shigar da Ma’aikatan sa kai cikin tsarin kiwon lafiya tare da sanya masu cutar kanjamau a cikin shirin bayar da gudummawar lafiya na jihar.

Karin karatu: Amurka ta musanta batun tallafawa ayyukan Boko Haram ta hannun USAID – Jakada

Ibrahim ya kara da bayyana kalubalen da masu karamin karfi ke fuskanta musamman marasa aikin yi da mazauna yankunan da ke da nisa, ya kuma yi gargadin cewa karancin maganin da ake fama da shi na iya haifar da matsalar rashin lafiya

Ya yi kira da a sake farfado da kwamitin tattara albarkatu na jihar Bauchi don tallafawa kudade da kula da marasa lafiya.

A nasa jawabin Dr Adamu Sambo, shugaban hukumar yaki da cutar HIV ta Jihar Bauchi (BACATMA) ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar na da shirin dorewa wajen bada magani kyauta.

Ya tabbatar da cewa ana samun magunguna a cibiyoyin jinya amma ya yarda cewa janyewar hukumar ta USAID ya yi tasiri wajen jefa al’umma cikin damuwa.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here