Wani dan sanda da ke aiki da rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Mohammed Alhaji Muhammad, ya mayar da kudi Naira Miliyan 2.6 da aka tura masa cikin asusun bankinsa bisa kuskure.
Da yake bayani kan dalilin mayar da kudin, Mohammed Alhaji Muhammad ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin gyara mummunar fahimta da wasu ke yi wa rundunar ‘yan sandan Najeriya a idon jama’a.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin.
Lamarin ya fara daukar hankalin jama’a ne bayan wani mai amfani da shafin Facebook, Bello Jafar, ya yaba wa dan sandan bisa gaskiya da rikon amana da ya nuna, inda ya bayyana shi a matsayin jami’in tsaro mai nagarta da amana ta musamman.
Bello Jafar ya bayyana cewa an tura kudin ne bisa kuskure daga wani kwastoman Moniepoint, amma dan sandan bai bata lokaci ba wajen daukar matakin da ya dace domin a mayar da kudin ga wanda ya dace.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno, Naziru Abdulmajeed, ya gayyaci dan sandan domin tattaunawa bayan samun labarin lamarin.
Ya bayyana cewa Mohammed Alhaji Muhammad, wanda ke aiki a sashen inshora na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ya samu sanarwar shigar kudin a wayarsa a ranar Alhamis, kuma nan take ya fahimci cewa bai yi tsammanin samun irin wannan kudi ba, inda a safiyar Juma’a ya nemi izini ya je bankinsa domin sanar da su kuskuren da aka yi da kuma bukatar a mayar da kudin yadda ya dace.













































