Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta koma harkokin koyo da koyarwa daga yau Alhamis, biyo bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shiga a fadin kasar.
SOLACEBASE ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa ta musamman mai dauke da sa hannun mukaddashin magatakardar jami’ar, Amina Umar Abdullahi a ranar Alhamis, za a ci gaba da jarrabawar zangon karatu na farko a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba. . 2023, bisa ga jadawalin jarrabawa.
Sai dai, ta ce duk jarrabawar da ta fado a cikin kwanakin yajin aikin (Talata, 14 zuwa Alhamis 16 ga Nuwamba, 2023), za a sake dagewa ne bayan jarrabawar karshe na jami’o’in.