Jami’ar Aliko Dangote ta kori ɗalibai 34, ta dakatar da wasu 13

KUST WUDIL

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a jihar Kano ta kori ɗalibai 34 saboda kama su da laifuka daban daban a lokacin jarrabawa.

Haka kuma, jami’ar ta dakatar da wasu ɗalibai 13 na tsawon zangon karatu guda, yayin da wasu kuma suka samu takardar gargadi daga hukumomin makarantar.

Wannan hukunci ya biyo bayan rahoton kwamitin dokokin jarrabawa da aikata ba daidai ba, wanda majalisar jami’ar ta amince da shi a zama na 123 da aka gudanar a ranar 9 ga Oktoba, 2025.

Kwamitin ya ba da shawarar matakai daban-daban na ladabtarwa ga ɗaliban da aka samu da laifin.

Shugaban sashen yaɗa labarai, wallafa da hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Abdullahi Datti, ne ya tabbatar da wannan bayani cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.

Ya ce, manufar hukuncin ita ce tabbatar da gaskiya da ɗa’a a harkokin jarrabawa.

A cikin rahoton, jami’ar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kare martabar tsarin karatu da tabbatar da cewa dalibai suna bin ka’idojin gudanar da jarrabawa yadda ya kamata.

Bugu da ƙari, jami’ar ta kafa Cibiyar Kula da Kayan Aiki domin inganta gyara da amfani da na’urorin bincike da koyarwa a dukkan sassan jami’ar.

Cibiyar za ta riƙa aiwatar da gyara kafin na’urori su lalace, tare da shirya horo ga malamai da ɗalibai kan yadda ake kula da kayan aiki.

Shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai, ya amince da naɗin Dakta Murtala Dambatta daga sashen Injiniya na Injin ɗin Mota a matsayin babban daraktan farko na cibiyar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here