Jami’an sintiri sun cafke ƴan Boko Haram titin zuwa Damboa

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Jami’an sintiri da ke gudanar da aikin tsaro na sa kai domin tallafa wa ayyukan sojoji a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, sun cafke wani ɗan ta’adda tare da wasu ƙarin mutane 3 waɗanda suka iske su suna rabon kayan amfanin gonar jama’a a mahaɗar titin Damaturu zuwa birnin Maiduguri.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa ƴan ta’addar sun mamaye gonakin wasu manoma yayin da suke ƙoƙarin kwashe kayan amfanin manoman.

Rahotonni sun ce, lamarin ya afku a maraicen ranar Laraba lokacin da masu gonakin 2 ke girbe kayan noman da suka samu a gonakinsu da ke kusa da ƙauyen Daiwa da ke titin Damboa.

Wata majiya ta rawaito cewa jagoran ƴan sintirin Saminu Audu na cewa “ƴan ta’addar sun harbe manoma tare da kashe mutum 2 da kuma jikkata mutum ɗaya”

“Sannan kuma bayan shan gumurzu kun ga an hallaka yan ta’adda guda 3, inda aka kama mutum ɗaya daga cikin su” inji shi.

Haka kuma ya ce, “Kuma waɗannan rukunin ƴan ta’addar na daga cikin ragowar Ƴan Boko Haram masu biyayya ga Abubakar Shekau da suka ƙi bada miƙa wuya ga tsagin yan ta’addar ISWAP”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here