Jami’an NDLEA sun cafke wata mata da ke shirin zuwa India a yi mata Tiyata ɗauke da ƙwayoyi

WhatsApp Image 2025 06 22 at 11.08.45

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wata mata mai shekara 43 Adekoya Adebukonla Mary da ta yi ikirarin tafiya kasar India domin yi mata tiyatar Karin Mahaifa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a birnin Lagos bayan da aka gano hodar ibilis mai nauyin kilo 2 digo 20 da aka saka a jakarta.

SolaceBase ta ruwaito cewa an kama wadda ake zargin ne a ranar Litinin, 16 ga watan nan da muke ciki na Yuni bisa ga sahihan bayanan sirri.

A karkashin sa ido, an ba Adekoya damar duba kayanta kuma an kama ta a lokacin da ta hau jirgin Qatar Airways zuwa India da zai bi ta Doha.

A lokacin da ake bincike kayanta, an gano wasu manya-manyan hodar ibilis kunshi biyu masu nauyin kilogiram 2 da 20 a boye a jikin bangon akwatin da take dauke da su.

A cikin bayaninta, ta yi ikirarin cewa ta fara wannan balaguron ne domin neman kudi amma bisa zargin cewa za ta je India domin a yi mata tiyata don cire mata Karin Mahaifa daga cikinta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta ce, a ranar Alhamis 19 ga watan Yuni jami’an NDLEA da sashen gudanar da bincike DOGI suka kama wani kampanin dakon kayayyaki da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1 da digo 3 da aka yi da su za su kai ta kasar Bahrain, yayin da a wani kamfanin jigilar kayayyaki a ranar Laraba 18 ga watan Yuni, wasu jami’ai 85 suka bankado wata rigar hodar Iblis a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni.

A jihar Bauchi, jami’an hukumar NDLEA da ke aiki da sahihan bayanan sirri a ranar Litinin 16 ga watan Yuni sun kama mutane biyun Ibrahim Galadima, mai shekaru 37 da Ibrahim Muhammed mai shekaru 28 a hanyar Bauchi zuwa Darazo, an cafke su da kwayoyi da kudinsu ya kai miliyan daya da dubu goma sha uku 1,013,000 inda kwayoyin suka kunshi opioids da tramadol da diazepam da exol-5.

A Kano, jami’an hukumar NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, sun kama Umar Hamisu, mai shekaru 19, da Dahiru Abdullahi, mai shekaru 32, inda aka same shi da kwayar skunk mai nauyin kilogiram 56 da digo 2, yayin da wani da ake zargi mai suna Obiwuru Henry, mai shekaru 27, shi ma aka kama shi a ranar da ampulun tramadol guda 23,720, da kuma penjougge 1,400.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here