Jami’an gwamnatin Ganduje suna rige-rigen ajiye muƙamansu

Ganduja Smiling
Ganduja Smiling

Kwamishinan ilimi a gwamnatin Ganduje Sunusi Saidu Kiru, ya yi murabus daga mukaminsa.

Haka kuma, babban mataimaki na musamman ga gwamna kan sa ido da tantancewa, Farouq Sule Garo, shi ma ya yi murabus daga mukaminsa domin ci gaba da fafutuka a harkokinsu na siyasa.

A cikin wasiƙar murabus ɗin da ya aike wa gwamnan, Sunusi Saidu Kiru, ya yaba wa gwamnatin ta Ganduje bisa damar da ta ba shi ta yin aiki a ƙunshin gwamnatin da kuma ƙwarin gwiwa da dudunmawar da gwamnatin ta ba shi a tsawon aikin da ya yi.

Idan dai za a iya tunawa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya umurci waɗanda ke son tsayawa takara a zaben baɗi da su yi murabus daga ranar 18 ga Afrilu ko kuma kafin ranar kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Sai dai kuma wasu kwamishinonin uku su ma sun miƙa takardar murabus din nasu da suka hada da, kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu Murtala Sule Garo sai kwamishinan raya karkara Musa Iliyasu Kwankwaso da takwaransa na kasafin kudi da tsare-tsare Nura Dankadai.

Sunusi Kiru ya ce, ya yi murabus ɗin nasa ne domin ya bashi damar tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Bebeji da Kiru a majalisar wakilai.

Haka zalika, Farouq Sule Garo a lokacin da yake godewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa ba shi damar yin aiki a matsayin babban mataimaki na musamman SSA don gudanar da ayyukansa a lokacin da ya ke rike da mukaminsa, ya ce ba za a iya kididdige irin kwarewar da cigaba da aikin nasa ya samar ba don haka yake godiya ga gwamnan.

Garo ya ce murabus ɗin nasa ya biyo bayan tsayawa takarar ɗan majalisar wakilai ta tarayya a mazaɓar Gwarzo da Kabo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here