Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta gargadi jama’a da su guji yada labaran karya na cewa ta na sauyawa dalibai cibiyoyin jarrabawa a maimakon garuruwan da suka zaba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dr Fabian Benjamin ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Asabar.
Benjamin ya bayyana cewa JAMB ta fahimci mahimmancin barin dalibi a yankin da ya zaba kuma tana tabbatar da cewa sun rubuta jarrabawar su a wuraren da suka zaba a cikin cibiyoyin yankin.
A cewarsa, kowane dan dalibi yana da hurumin zabar garin da yake son rubuta jarrabawar, kuma hukumar JAMB ta sanya shi wata cibiya dake cikin garin.
Karin karatu: Za a sake bude filin jirgin saman Enugu bayan gyaran titin jirgin – FAAN
A cewar JAMB Ikirarin da ba shi da tushe balle makama na cewa ana tura dalibai zuwa garuruwa daban-daban da abin da suka zaba, kuskure ne, zalunci ne, da nufin bata sunan Hukumar ne kawai, hakan ba ya faruwa. (NAN)