Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya rasu – Kafafen yaɗa labaran gwamnati

1x 1 750x430

Gwamnatin Iran ta sanar a ranar Lahadi cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan ƙasar sun yi ajalin Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya shafe shekaru yana jagorantar ƙasar a matsayin Jagoran Addini kuma babban maƙiyin Isra’ila da Amurka.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da rasuwar jagoran sa’o’i kaɗan kafin haka, tare da kira ga ‘yan Iran da su karɓi ragamar mulkin ƙasarsu.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran ya tabbatar da rasuwar a safiyar Lahadi, yayin da yaƙin ya shiga rana ta biyu tare da sabbin hare-hare kan ƙasar.

Rahotanni sun ce ya rasu ne a ofishinsa da ke gidansa sakamakon wani hari da aka kai da safiyar Asabar.

Rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps ta yi alƙawarin ɗaukar fansa kan abin da ta kira hare-haren Amurka da Isra’ila.

Har yanzu ba a bayyana ko hare-haren Amurka ne ko na Isra’ila suka yi sanadin mutuwar jagoran ba, haka kuma ba a fayyace wanda zai jagoranci ƙasar gaba ɗaya ba.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya ce shugaban ƙasa, shugaban ɓangaren shari’a da kuma wani masani a Majalisar Guardian Council za su riƙe ragamar mulki a lokacin miƙa mulki, kamar yadda wani babban ɗan siyasa, Mohammed Mokhber, ya bayyana.

Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe wasu manyan jami’ai a tsarin shugabancin Iran, sai dai ba a san ko cire Khamenei, mai shekaru 86, zai kawo gagarumin sauyi a tsarin da ya jagoranta ba.

Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun bayyana cewa sauya gwamnati na daga cikin manufofin hare-haren da aka fara da misalin ƙarfe 1:00 na daren Asabar agogon ƙasar.

Trump ya ce wa ‘yan Iran su karɓi ragamar mulki bayan an kammala hare-haren.

Rasuwar jagoran na Iran na ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da ka iya haifar da ruɗani da gibin iko a yankin da tuni ke fama da tashin hankali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here