Injiniya Habu Ringim ya karɓi lambar yabo daga ƙungiyar SCIAN a Kano

WhatsApp Image 2025 09 21 at 12.32.22 750x430

Ƙungiyar masu fama da lalurar Laka ta Najeriya (SCIAN), reshen Kano, ta karrama Injiniya Mustapha Habu Ringim, wanda ya kafa gidauniyar ENGAUSA, da lambar yabo ta sana’o’i ta SCIAN 2025.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa an bai wa Injiniya Ringim wannan lamba ne saboda gagarumin nasarorin da ya samu a fannin ilimi, jajircewarsa wajen inganta harkar ilimi, da kuma gudummawarsa ga walwalar masu nakasa.

An mika masa wannan lambar yabo a wajen bikin tunawa da Ranar masu fama da lalurar Laka ta duniya da aka gudanar a Meena Event Centre, Kano, ranar Asabar.

Shugaban ƙungiyar SCIAN reshen Kano, Abdulrahman Uba Daushe, ya bayyana cewa lambar yabo ta musamman ce domin girmama ƙoƙarin Injiniya Ringim wajen tallafa wa ilimi da kuma shirye-shiryen ci gaban masu nakasa.

Ya ƙara da cewa, “Muna murnar wannan rana tare da karrama Injiniya Ringim bisa gagarumar gudummawarsa da ta zama abin koyi a al’umma.”

Bayan karɓar lambar, Injiniya Ringim ya nuna farin ciki da mamaki, yana mai cewa wannan karramawa ta zo masa a bazata.

Ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen bayar da gudummawa a fannin ilimi da ci gaban ɗan Adam musamman ga masu nakasa.

Ƙungiyar SCIAN, reshen Kano, wadda taken ta shi ne “Ƙalubalantar Iyakokinmu,” na ci gaba da wayar da kai tare da shirye-shiryen tallafi da lambar yabo ga masu raunin ƙashin baya domin inganta rayuwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here