Kwamishinan zabe na INEC a Akwa Ibom, Dr Cyril Omorogbe ya ce hukumar ta soke sunayen ma’aikatan zaɓe na wucin-gadi guda 100 a jihar bisa zargin hannu a cikin maguɗin zaɓe.
Omorogbe ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Uyo a jiya Alhamis.
Ya ce an samu ma’aikatan wucin-gadin da abin ya shafa da laifin tafka maguɗin zaɓe a lokacin zaɓen shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a jihar.
“Mun soke sunayen su, ba za mu yi amfani da su ba a lokacin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar,” inji shi.
Kwamishinan zaben ya ce hukumar ta fara raba wasu muhimman kayayyakin zaɓe ga kananan hukumomin jihar gabanin zaben ranar gobe Asabar.
Omorogbe ya ce, an yi dukkan shirye-shirye domin tabbatar da isar kayan aiki da ma’aikatan da za su gudanar da zabe da wuri.