INEC ta bayyana Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Gwamnan jihar Anambra

Soludo 750x430

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Farfesa Chukwuma Soludo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025.

Farfesa Edoba Omoregie, wanda shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓen na jihar, ne ya sanar da nasarar Soludo a hedikwatar INEC da ke Awka a ranar Lahadi.

Soludo ya samu ƙuri’u 422,664, inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nicholas Ukachukwu, wanda ya samu ƙuri’u 99,445. Ɗan takarar jam’iyyar Young Progressives Party (YPP), Sir Paul Chukwuma, ya zo na uku da ƙuri’u 37,753.

A cewar INEC, jam’iyyu 16 ne suka tsayar da ‘yan takara a wannan zaɓe.

Jimillar masu kaɗa ƙuri’a da aka yi wa rijista a jihar ita ce 2,788,864, amma guda 598,229 ne aka tantance, sai kuma adadin ƙuri’un da aka kaɗa ya kai 595,298, inda aka soke ƙuri’u 11,244 a faɗin ƙananan hukumomi 21 na jihar.

Daga sakamakon da aka sanar, Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe dukkan ƙananan hukumomi 21 da ke cikin jihar Anambra cikin babbar nasara.

Farfesa Omoregie ya bayyana cewa, “Adadin ƙuri’un da suka inganta sun kai 584,054, yayin da aka soke 11,244, wanda ya haifar da jimillar ƙuri’u 595,298.”

Ya ƙara da cewa akwai wasu wurare da aka samu matsaloli a cikin ƙananan hukumomi kamar Anambra ta Gabas, Anaocha, Awka ta Yamma, da Onitsha ta Yamma, inda aka soke ƙuri’u 10,481, amma hakan bai shafi sakamakon ƙarshe ba.

Ya ce, “Ni Farfesa Edoba Omoregie, jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Anambra na shekarar 2025, na bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali. Don haka, Chukwuma Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, wanda ya samu ƙuri’u 422,664 — mafi girma cikin sahihan ƙuri’un da aka kaɗa, kuma ya cika sharuddan doka, don an bayyana shi a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaɓen.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here