IGP ya kafa tawagar sa-ido don daƙile rashin tsaro lokacin zaɓe

IGP alkali
IGP alkali

Sufeto-Janar na Ƴansanda, IGP, Usman Baba, ya amince da kafa tawagar tsare-tsare, sa ido da nazari a kan zabe gabanin babban zabe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

Ya ce za a baza ƴan tawagar a fadin jihohin tarayyar kasar domin tantancewa da kuma daƙile matsalolin tsaro a lokacin zabe.

Adejobi ya ce tawagar za ta gudanar da aikin tantancewa tare da tantance matsugunan tsaro a gabanin babban zabe.

Ya ce kafa wannan tawaga wani ɓangare ne na yunƙurin IGP na tabbatar da tsaro da amintaccen zaɓe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here