Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ta fara sabon bincike kan zargin karkatar da sama da naira biliyan huɗu daga kuɗin jihar zuwa aikin tashar Tsandauri ta Dala, bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta cire hannun karin jihar daga kamfanin.
Rahotanni sun ce sama da naira biliyan huɗun an kashe su wajen bayar da kwangilar samar da kayayyakin more rayuwa ga aikin tashar, jim kaɗan bayan da aka maida kaso 20% na jarin jihar da ke cikin kamfanin zuwa hannun iyalin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 2020.
Wannan mataki ya sa jihar Kano ta rasa matsayin ta na mai mallakar kaso a aikin, inda kuma ’ya’yan tsohon gwamnan suka zama daraktoci da masu hannun jari a kamfanin.
Rahotanni sun nuna cewa lokacin da aka bayar da kwangilar, jihar ba ta sake kasancewa cikin masu hannun jari ba a ciki ba.
Labari mai alaƙa: Yadda ake zargin Ganduje ya kwace hannun jarin Kano a tashar Tsandauri
Wani binciken jaridar PREMIUM TIMES ya nuna cewa kaso na jihar Kano a tashar Tsandauri ta Dala an mayar da shi ga tsohon gwamnan da iyalinsa yayin mulkinsa, lamarin da ya haifar da korafe-korafe da dama daga jama’a.
Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin Hanci ta jihar Kano, Sa’idu Yahya, ya tabbatar da cewa binciken ya kai matakin karshe kuma ana daf da kammalawa.
Ya ce sun karɓi korafe-korafe daga jama’a, inda aka gayyaci mutane da dama da ake zargi, ɗaya daga cikinsu ma aka kama amma daga bisani aka bayar da belinsa bayan ya bayar da muhimman bayanai.
Ya ƙara da cewa bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi yanzu yana garin Yola a Jihar Adamawa, kuma bayan kammala binciken za a gurfanar da su a kotu, domin an samu hujjoji masu ƙarfi da ke tabbatar da zargin karkatar da kuɗaɗen jihar.













































