Hukumar tattara haraji ta ƙasa FIRS ta rasa manyan ma’aikata hudu sakamakon gobara a Legas

1758129527866

Hukumar tatara haraji ta ƙasa (FIRS) ta shiga jimami bayan rasuwar manyan ma’aikata hudu a wani mummunan gobara da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad, Legas, a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatan sun makale ne a ofishin FIRS guda biyu da ke bene na shida da na bakwai a ginin, lokacin da wutar ta tashi ba tare da an sami damar ceto su ba.

A cikin wata sanarwa da mai ba wa shugaban FIRS shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dare Adekanmbi, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana sunayen wadanda suka rasu da cewa su ne: Hajiya Ekelikhostse George, mataimakiyar darekta; Malam David Sunday-Jatto, mataimakiyar darekta; Hajiya Nkem Onyemelukwe, babban manaja; da kuma Malam Peter Ifaranmaye, manaja.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaro da na kiyaye lafiya na FIRS sun gaggauta kiran jami’an kashe gobara bayan da suka samu labarin, amma zuwa lokacin da suka isa wurin, hayaki mai kauri ya riga ya turnuƙe ginin.

Hukumar ta bayyana cewa dukkan shugabanni da ma’aikatan FIRS suna cikin alhini da baƙin ciki tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da alƙawarin bayar da cikakken tallafi a wannan mawuyacin lokaci.

Haka kuma an tabbatar da cewa za a ɗauki matakan ƙara tsaurara tsaro da hanyoyin kariya a dukkan ofisoshin hukumar a fadin ƙasar.

A halin yanzu, jami’an agajin gaggawa sun tabbatar da cewa bincike ya fara domin gano ainihin musabbabin gobarar, lamarin da shaidu suka ce ya bazu cikin ginin mai hawa da yawa cikin gaggawa, inda ya rutsa da masu aiki a bene daban-daban.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here