Shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya yi Allah wadai da ɗibar ganimar Mai daga tankar dakon fetur da ta fadi a Apapa da ke jihar Legas, yana bayyana hakan a matsayin mummunan aiki da ke barazana ga rayukan jama’a da tsaron al’umma.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na NOA, Bala Musa, hukumar ya fitar a Abuja, inda ya bayyana cewa ya zama wajibi majalisar tarayya ta ɗauki matakin doka domin mayar da ɗibar Mai daga tankar da ta fadi a matsayin laifi, tare da tanadin hukunci mai tsauri.
Hukumar ta nuna cewa wannan dabi’a ba ta dace da zamani ba, domin tana jefa rayukan mutane cikin haɗari mai tsanani da kuma lalata muhimman ababen more rayuwar ƙasa, inda barazanar ba wai masu ɗibar man kawai ta ke shafa ba, har da masu ababen hawa, al’ummomin da ke kusa, jami’an ceto da kuma muhimman kadarorin gwamnati.
NOA ta jaddada cewa tsawon shekaru tana aiwatar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a a fadin ƙasa domin ilmantar da ‘yan Nijeriya kan hatsarin ɗibar Mai da sauran halaye masu haɗari, amma duk da haka wasu na ci gaba da aikata wannan aiki mai kashe rayuka.
Hukumar ta bayyana cewa talauci ba hujja ba ce ta aikata abin da ke barazana ga rayuwa, tare da bayyana ɗibar mai a matsayin aikin ganganci da sakaci da rayukan mutane da tsaron jama’a.
Issa-Onilu ya tunatar da irin bala’o’in da suka faru a baya sakamakon haɗurran tankokin mai da ɗibar man, inda fashe-fashe suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
Ya bukaci majalisar tarayya ta kafa dokar da za ta haramta ɗibar mayi daga tankokin da suka fadi, tare da hukunci mai tsauri domin hana aikata laifin.
NAN













































