Hukumar NDE ta ƙaddamar da shirin ɗaukar sabbin ma’aikata

NDE

Hukumar Samar da ayyukan yi ta Najeriya NDE, ta ƙaddamar da kashi na biyu na shirin Renewed Hope Employment Initiative, wanda ya shafi ɗaukar sabbin ma”aikata ƴan Najeriya 27,000 marasa aikin yi a jihohi 36 da kuma birnin tarayya Abuja.

A yayin kaddamar da shafin Intanet na aikace-aikacen ɗaukar aikin ranar Litinin a Abuja, babban Daraktan hukumar ta NDE, Silas Agara, ya ce, shafin wanda yanzu ya aka kammala shirya shi kaso 100 bisa 100 an gina shi ne kan nasarori da darussa da aka samu a kashi na farko, wanda aka kaddamar a shekarar 2024, aka kuma kammala bikin yaye wadanda suka ci gajiyar shirin a watan Maris din bana.

Agara, wanda shi ma ya buɗe shafin domin gwada yin rajista, ya ce, an fara cike neman shiga cikin shirin ne daga ranar Litinin 28 ga watan Yuli zuwa ranar Litinin 11 ga watan Agusta, 2025.

Za a fara horaswa da gudanar da aikace-aikacen tsakanin 12 zuwa 22 ga Agusta, tare da aiwatar da cikakken aiwatar da hoeon a farkon watan Satumba.

Haka kuma ya ƙara da cewa kashi na biyu na shirin ya fadada cancanta ga matasa masu shekaru daga 18 zuwa 45, daga shekarun 18 zuwa 35 da aka yi amfani da su a kashin farko.

A cewarsa, masu neman cin gajiyar shirin dole ne su kasance suna da Lambar shaidar zama ɗan ƙasa NIN sannan su nema bisa yanayin zamansu, ba wai asalinsu ba.

Agara ya jaddada hada kai, inda ya bayyana cewa shirin ya kunshi mutane masu ilimi daban-daban, ciki har da waɗanda suka kammala karatun sakandare, da da kuma wadanda suka kammala karatunsu ba su da kwarewar aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here