Hukumar NAFDAC za ta ɗauki sabbin ma’aikata 1,000

NAFDAC Abuja 1 750x420

Gwamnatin tarayya ta amince da ɗaukar sabbin ma’aikata dubu ɗaya a hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) domin ƙarfafa aikin sa ido da aiwatar da dokokin da suka shafi kayayyakin abinci da magunguna a ƙasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta sanar da haramta samarwa, sayarwa da rarraba giya da aka saka a cikin ƙananan kwalabe ko roba da ba su kai milimita 200 ba, da kuma giya a cikin jakunkuna.

Haramcin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairu, 2026, domin rage yawan shan giya da kare lafiyar jama’a, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja, inda ta ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin ma’aikatar lafiya ta tarayya da kuma kudirin majalisar dattawa.

Ta bayyana cewa manufar ita ce kare yara, matasa da masu tasowa daga illolin giya mai rahusa da ake iya samu cikin sauƙi, wadda ke ƙara yawan barna a cikin al’umma.

Farfesa Adeyeye ta jaddada cewa irin wannan giya tana taimakawa wajen ƙara yawan hatsarori a hanya, tashin hankali a gida, da kuma barin makaranta da wasu matsalolin zamantakewa.

Karanta: Tsofaffin Sojoji sun soki Wike kan rikicinsa da jami’in Sojan ruwa, sun buƙaci ya bada haƙuri

Ta ce an ɗauki wannan mataki ba don cutar da wani ba, sai dai don kare lafiyar al’umma, inda ta ƙara da cewa ba za a musanya lafiyar jama’a da ribar tattalin arziki na ɗan lokaci ba.

Haramcin dai zai shafi giya mai ƙarfi (spirit drinks) da ke cikin ƙananan kwalabe da jakunkuna kawai, ba dukkanin nau’o’in giya ba.

A baya hukumar ta NAFDAC ta amince da haɗin gwiwa da masana’antar giya domin a daina irin wannan marufi tun a 2024, amma ta tsawaita wa’adin zuwa Disamba 2025 don ba kamfanoni damar daidaita ayyukansu.

Hukumar ta ce wannan mataki yana cikin kudirin Najeriya na bin tsarin hukumar lafiya ta duniya (WHO) wajen rage amfani da giya mai illa, kuma ta yi kira ga dukkan masu samarwa da dillalai da su bi doka kafin ƙarshen wa’adin 2025, domin ba za a ƙara wa’adi ba.

Hukumar NAFDAC za ta yi aiki tare da ma’aikatar lafiya, hukumar kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), da hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) don wayar da kan al’umma game da illolin shan giya fiye da kima.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here