Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) ta musanta zargin da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi cewa jami’an hukumar sun kwace mata fasfo a filin jirgin sama.
Mai magana da yawun hukumar, Akinsola Akinlabi, ya bayyana cewa abin da ya faru a filin jirgin sama wata hanya ce ta duba takardu da ake bi na yau da kullum, ba kwace fasfo ba.
Ya ce jami’an hukumar suna da ikon ɗaukar fasfo na ɗan lokaci domin yin bincike kafin su mayar da shi, kuma hakan ba yana nufin an kwace shi bane kamar yadda ake ikirari.
Akinlabi ya ƙara da cewa an ba sanatar damar tafiya bayan an kammala bincike, yana mai cewa bidiyon da ta wallafa a kafar sada zumunta an ɗauke shi ne yayin da ake cikin tsarin bincike, ba bayan an gama ba.
Labari mai alaƙa: Jami’an hukumar kula da shige da fice suk kwace fasfo ɗin Sanata Natasha a filin jirgi
A cewar shi, Sanata Natasha ta yi zaton an hana ta tafiya ne yayin da ake duba takardunta, amma daga baya an mayar mata da fasfon nata kuma ta ci gaba da tafiya.
Tun da fari dai Sanata Natasha ta zargi jami’an hukumar kula da shige da fice da hana ta fita ƙasar waje, inda ta yi zanga-zanga ta kai tsaye ta kafar Facebook tana cewa an kwace mata fasfo ba tare da wata hujja ta doka ba.
Sai dai daga baya, bayan tattaunawa, jami’an suka dawo mata da fasfon nata, inda aka ji tana cewa da ba ta yi magana a fili ba, da ba za a mayar mata da takardarta ba.













































