Hukumar kula da lafiya da kai ɗaukin gaggawa NEMSAS , wato National Emergency Medical Services and Ambulance System (NEMSAS), ta faɗaɗa ayyukanta zuwa jihohi 30 a faɗin ƙasar nan, domin bai wa mazauna waɗannan jihohin damar samun kulawar gaggawa kyauta ta hanyar kiran lambar 112.
Shugaban shirye-shiryen hukumar na ƙasa NEMSAS, Dakta Emuren Doubra, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, a ranar Lahadi a birnin Abuja.
Doubra ya ce, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ɗaukar nauyin kulawar gaggawa ta awanni 48 na farko, wanda ake biya daga asusun kula da lafiya na asali, wato Basic Health Care Provision Fund (BHCPF).
Ya bayyana cewa an samu ci gaba mai yawa, inda aka ƙara yawan jihohin da suka shiga cikin tsarin da kashi 25 bisa ɗari, tare da ƙaruwa da kashi 304 cikin ɗari na yawan masu cin gajiyar kulawar gaggawa.
Ya ce, adadin marasa lafiya da aka kai asibiti ya ƙaru daga ƙasa da mutum 3,000 zuwa sama da 11,000, wanda ke nuna yadda ake samun saurin amsa kiran gaggawa da kuma haɗin kai tsakanin cibiyoyi a matakai daban-daban.
Ya bayyana cewa, NEMSAS ta raba fiye da naira miliyan 487 ga jihohi da cibiyoyi a zangon uku na wannan shekara, inda naira miliyan 332.6 suka tafi manyan asibitoci, sannan naira miliyan 154.3 suka tafi ga jihohi da suka haɗa da Yobe, Ribas, Ebonyi, Gombe, Ogun, Bayelsa, Osun, Bauchi da Anambra.
Doubra ya ce, an ƙirƙiri tsarin SAVEMAMA da ke amfani da lambar 3581, wanda ke bai wa mata masu juna biyu damar neman taimakon gaggawa ta hanyar kira ko sakon rubutu kyauta ba tare da amfani da kuɗin kira ba.
Ya ƙara da cewa, NEMSAS ta haɗa kai da hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) domin amfani da motocin asibiti na “Zebra” da kuma horas da jami’anta kan taimakon gaggawa, musamman ga mata masu juna biyu da jarirai.
Ya ce, hukumar na ƙoƙarin tabbatar da cewa babu ɗan ƙasa da zai rasa rayuwa saboda jinkirin samun taimako a lokacin da za a iya cetonsa da sauri.
NAN













































