Babban Kwamandan hukumar kiyaye hadurran ta ƙasa (FRSC), Malam Shehu Mohammed, ya amince da sake tura wasu manyan jami’an hukumar domin inganta ayyuka a fadin kasar.
A cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na FRSC, Olusegun Ogungbemide, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, an bayyana cewa sabon sauyin ya shafi mukamai da dama ciki har da sabon Sakatare Janar na hukumar, mataimakan kwamanda guda hudu (ACMs), da kuma kwamandojin jihohi.
Mohammed ya ce wannan sauyi na cikin matakan kara wa hukumar kuzari wajen gudanar da aikinta da kuma tabbatar da tsaro a kan tituna.
Sabon sakatare janar shi ne ACM G. Ntukidem, yayin da ACM J.W. Toby ya koma Kwamandan shiyya a Osogbo.
Haka kuma, ACM I. Abubakar da ACM A.M. Hassan sun karbi sabbin mukamai a babban ofishin Abuja.
Haka nan, ACM A. Sanusi wanda ya kammala karatu a Kwalejin horar da ayyukan tsaro ta kasa ya karbi ragamar kula da sashen koyar da ma’aikata.
Sauyin ya shafi kwamandojin jihohi da dama, inda CC J.N. Alexander ya koma daga Anambra zuwa Delta, CC Y.T. Etuku daga Kebbi zuwa Kogi, sannan wasu jami’ai sun samu sabbin wuraren aiki a Abia, Anambra, Kebbi, Bauchi da Yobe.
Gaba ɗaya, jami’ai 61 ne aka sake musu wurin aiki a sassa daban-daban na hukumar, ciki har da babban ofishin kasa, makarantar koyon aiki, cibiyoyin yanki, da sassa na musamman.
Babban kwamandan ya ce wannan canjin zai taimaka wajen kara karfin aiki, tsari, da kuma inganta ayyukan hukumar musamman a fannonin kula da hanya, dabarun gudanarwa, bincike, koyarwa, da ayyukan lafiya.
Ya bukaci sabbin jami’an su yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da tsaro da bin dokokin hanya a fadin Najeriya.
NAN













































