Hukumar kiyaye abkuwar haɗɗura ta ƙasa ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a hatsarin mota a Zamfara

WhatsApp Image 2025 09 13 at 19.06.38 750x430

Hukumar kiyaye abkuwar haɗɗura ta ƙasa reshen jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane 17 sakamakon hatsarin mota da ya auku bayan wata motar haya ta yi karo da gada da ta ruguje a yankin Gwalli na jihar.

A cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, Isah Aliyu, ya fitar a Gusau ranar Litinin, ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu mata ne, lokacin da motar daukar fasinjoji mai kujeru 18 ta yi karo da gadar da ta rushe lokacin da take gudu.

Aliyu ya ce gadar ta ruguje a cikin makon nan, lamarin da ya tilasta mazauna yankin amfani da jakunkunan kasa domin motoci su ratsa.

Sai dai direban motar ya kasa lura, inda ya shiga cikin ruwan gadar da ya karya, abin da ya jawo asarar rayuka.

Ya kuma ambato kwamandan hukumar a jihar, Aliyu Ma’aji, wanda ya nuna bakin ciki da jimami bisa wannan mummunan lamari, tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, gwamnatin jihar da kuma al’ummar Zamfara baki daya.

Labari mai alaƙa: Mahalarta ɗaurin aure 19 sun rasu sakamakon rushewar gada a Zamfara

Ma’aji ya shawarci direbobi da su guji yin tafiya cikin dare da kuma yin tuki da nauyin da ya wuce kima.

Ya kuma bukace su rika neman bayanai kan yanayin hanyoyi kafin fara doguwar tafiya.

Haka zalika, kwamandan ya yaba wa hukumomi da al’umma da suka taimaka wajen ceto wasu daga cikin wadanda suka tsira daga hatsarin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani hatsari a jihar inda mutum 19 suka mutu sakamakon rushewar wata gada a wurin da ake bukin aure.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here