Kwamitin, wanda aka kafa shi a lokacin zanga-zangar ƙin jinin ayyukan rundunar ƴan sanda mai yaƙi da fashi da makami ta Sars, bai faɗi adadin jami’an ƴan sandan da yake so a kora ko a gurfanar da su a gaban kotu ba, amma za a bayyana wa jama’a hakan a nan gaba.
Kwamitin ƙarƙashin wani babban alƙali Sulaiman Galadima ya kuma umarci a biya diyya ga ƙarin mutanen da ƴan sanda suka azabtar.
A farkon watan nan ne aka biya gwamman waɗanda abin ya shafa da iyalansu diyya ta jumullar kusan dala 700,000 – a karon farko da aka bayar da irin ta tun kafa kwamitin.
Kusan shekara biyu kenan da aka gudanar da gagarumar zan-zangar EndSars ta adawa da rundunar yaƙi da fashi da makai ta ƴan sanda a Najeriya.
Masu zanga-zangar sun tursasa wa hukumomi soke sashen Sars – wanda aka ƙirƙira don yaƙi da fashi da makami da satar mutane don neman kuɗin fansa.
Zanga-zangar ta EndSARS wadda aka fara a Legas da Abuja a watan Oktoban 2020, ta kuma fantsama zuwa wasu jihohin kasar, kafin daga bisani ta rikiɗe ta koma rikici, abun da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wasu ɓata gari da ake zargin sun fake da zanga-zangar sun rika rusa gine-ginen gwamnati da na wasu ‘yan siyasa musamman a jihar Legas, da ke kudu maso yammacin kasar.
Hukumomi sun baza jami’an ƴan sandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin, sai dai tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa sakamakon kisan masu zanga-zanga a Lekki.
Masu zanga-zangar sun zargi jami’an tsaro da buɗe masu wuta a Lekki da ke jihar Legas, wato cibiyar inda ake gudanar da zanga-zanar, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.
Wasu dai na ganin buɗewa masu zanga-zangar wuta ya taimaka wajen kazantuwar lamarin musamman a jihar ta Legas.
Zanga-zangar ta ja hankalin duniya sosai inda har shahararrun mutane a fadin duniya suka dinga tsoma baki suna nuna goyon baya ga masu yin ta.