Hukumar ICPC ta dawo da Naira biliyan 446, ta kuma dakatar da yunƙurin wawurw Naira biliyan 142 – hukumar NOA

ICPC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (ICPC) ta bayyana cewa ta dawo da sama da Naira biliyan 446 tare da dakatar da Naira biliyan 142 daga wawurewa, da kuma Naira biliyan 30 a cikin wata guda.

Daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), Malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin taron sanarwar tsaro na ƙasa da ake gudanarwa kowane wata a birnin Abuja.

Ya ce hukumar ICPC ta samu babban nasara a watan Satumba wajen yaki da cin hanci a ƙasar nan.

Issa-Onilu ya bayyana cewa hukumar ta karɓi korafe-korafe 19 daga jama’a ta hanyoyin kai tsaye da na yanar gizo, inda daga cikin shari’o’i 33 da aka ba ta, ta kammala bincike a kan tara kuma ta samu hukunci na laifi guda uku.

Karanta: Hukumar NERC ta fara bincike kan kamfanonin rarraba wutar lantarki bayan ma’aikata 38 sun mutu a bakin aiki

Haka kuma, hukumar ta gudanar da taruka da bitoci 77 na wayar da kai kan yaki da cin hanci, inda mutane 41,922 suka amfana da su, ciki har da lauyoyin gwamnoni na jihohi.

Ta kuma gudanar da nazarin tsarin aiki da tantance haɗarin cin hanci a wasu hukumomi tare da kafa ƙungiyoyin gaskiya da rikon amana guda takwas a wasu ma’aikatun gwamnati domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

Hukumar ICPC ta kuma kara yawan hulɗarta ta internet zuwa saƙonni 1,650, tare da watsa shirye-shiryenta guda huɗu na talabijin mai taken Transparency Files a harshen Turanci, da kuma shirye-shirye 27 na harshen gida a sassa daban-daban na ƙasar.

Bugu da ƙari, hukumar ta fitar da sanarwa 12 na labarai, waɗanda suka samu wallafa 121 daga kafafen yada labarai daban-daban.

Wannan aiki, a cewar Issa-Onilu, na nuna jajircewar hukumar ICPC wajen tabbatar da gaskiya, amana da ƙasa mai tsabta daga cin hanci da rashawa.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here