Hukumar gudanarwa ta sanar da ƙarin girma ga manyan jami’an tsaro 24,202

Paramilitary Board 750x430

Hukumar gudanarwar tsaro ta Civil Depence da ta gyaran hali da ta kashe gobara da hukumar kula da shige da fice (CDCFIB)  sanar da karin girma ga manyan jami’ai 24,202 a cikin manyan hukumomin tsaro guda huɗu.

Ministan harkokin cikin gida kuma shugaban hukumar Olubunmi Tunji-Ojo, ta bakin sakataran hukumar Abdulmalik Jubril, ya bayyana karin girman yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da hukumar gyaran hali ta ƙasa NCoS, hukumar shige da fice ta ƙasa NIS, hukumar kashe gobara ta tarayya FFS, da kuma hukumar tsaro ta Civil Depence NSCDC.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa cikin jami’an da aka kara wa girma, NCoS ta samu 11,426, NIS ta samu 4,336, FFS ta samu 2,581, yayin da NSCDC ta samu karin jami’ai 5,859.

Ya ce an yi karin girman bisa la’akari da wasu muhimman ka’idoji da suka haɗa da rarraba mukamai a fadin ƙasa, tarihin aiki na jami’an, tantancewa, tasirin aiki da kuma kujerun da ake dasu.

Ministan ya kara da cewa wannan karin girma na nufin ƙarfafa gwiwar jami’an domin inganta aikin da suke yi a hukumominsu.

Ya bayyana cewa hakan ya yi daidai da tsarin shugaban ƙasa Bola Tinubu na inganta walwalar ma’aikata a karkashin shirin farfadowa da ake kira Renewed Hope Agenda.

Ya ce a baya karin girma ya tsaya cak, amma wannan gwamnati ta dage wajen inganta walwalar jami’an domin su yi aiki tukuru wajen yakar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here