Shugaban Hukumar tattara haraji ta Najeriya FIRS, Zacch Adedeji, ya ba da umarnin tsawaita ayyukan ofisoshin haraji har zuwa ranakun ƙarshen mako na watan Yuni.
Adedeji ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa da mai bai wa shugaban FIRS shawara kan harkokin yada labarai Dare Adekanmbi, ya fitar.
A cewar Adekambi, ya na daga cikin ƙudurin da Adedeji ya yi na daidaita manufofin hukumar da abokan hulɗarsu da Kuma ayyukan da suke gudanarwa.
“Taron karshen makon, wanda aka fara a ranar 14 ga watan Yuni, zai ƙare ranar Lahadi 29 ga watan Yuni.
“An yi haka ne don taimaka wa kamfanonin da doka ta ba su damar shigar da bayanan harajin su a karshen wata don cika wa’adin,” in ji shi.
“Kamar yadda kuka sani, watan Yuni shi ne kololuwar lokacin shigar da harajin Kamfanoni na shekara-shekara.
“Masu biyan haraji da yawa wadanda shekarar kudi ta kare a ranar 31 ga Disamba, ana sa ran za su gabatar da bayanan harajin su nan da 30 ga watan Yuni.
(NAN)













































