Hukumar ba da agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin Duniya za ta rufe ayyukanta a Najeriya

UNHCR 750x430

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (UNOCHA) zai rufe ayyukansa a Najeriya.

Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Farfesa Nentawe Goshwe, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin wani taron tabbatar da tsarin da za a dauka a Najeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, kuma ofishin mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Abuja.

A cewarsa, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, Mohamed Fall, ya sanar da shi game da matakin.

Farfesa Nantawe, wanda ya koka kan yadda bala’o’in ambaliyar ruwa da rashin tsaro ke barazana da rayuwa a Najeriya, inda ya yabawa hukumar ta UNOCHA a kan ayyukan da take yi a kasar, musamman a jihohin Arewa maso Gabas da ke fama da rikici.

Ya bayyana matakin da abin takaici da hukumar UNOCHA ta dauka na ficewa daga Najeriyar sakamakon kalubalen jin kai da har yanzu ake fuskanta a fadin kasar.

Karanta: Matatar man Dangote ta sake rage Farashin man fetur

Sai dai Farfesa Goshwe ya jaddada kudirin shugaban kasa Bola Tinubu na magance matsalar ambaliyar ruwa da sauran bala’o’i a kasar.

Tun da farko, hukumar ba da agajin gaggawa rage bala’o’i ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta rage yawan ma’aikatanta a duniya da kashi 20 cikin 100 sannan za ta rage ayyukanta a kasashe tara, yayin da take fuskantar matsalar kudade da kuma karuwar bukatun duniya.

A wata wasika da ya aike wa ma’aikatan da aka wallafa a internet ranar Juma’a, shugaban ofishin kula da harkokin jin kai (OCHA) Tom Fletcher ya bayyana rage ayyukan sakamakon gibin kudade na kusan dala miliyan 60 na shekarar 2025, tare da karuwar bukatun jin kai.

OCHA za ta janye daga ko daidaita ayyuka a Kamaru, Kolombiya, Eritrea, Iraq, Libya, Nigeria, Pakistan, Turkey, da Zimbabwe.

Hukumar na shirin korar ma’aikatanta kusan 500 daga cikin ma’aikatanta kusan 2,600 a cikin kasashe sama da 60 da ke da yawan matsuguni a wurare kadan, a cewar Najwa Mekki, daraktan sadarwa a OCHA yana ambaton wata wasika ta daban da Fletcher ya rubuta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here