Hukumar ƴan sandan ƙasa da ƙasa “Interpol” ta tabbatar da cafke manyan ƴan Ta’adda 11 a Najeriya

Interpol 1 750x430

Hukumar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa wato Interpol, ta tabbatar da kama manyan membobi 11 na ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya.

Wannan samame ya kasance wani ɓangare na aikin da aka kira “Operation Catalyst”, wanda aka kaddamar don dakile hanyoyin samun kuɗin ta’addanci da laifukan da ke da alaƙa da su a ƙasashe shida na Afirka.

Interpol ta bayyana cewa aikin, wanda ya gudana daga watan Yuli zuwa Satumba 2025, ya haifar da kama mutane 83 da kuma gano wasu mutane 160 da ake bincike a kansu.

Ƙasashen da suka halarci aikin sun haɗa da Najeriya, Angola, Kamaru, Kenya, Namibiya da Sudan ta Kudu.

A Najeriya, hukumar ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da ta’addanci, ciki har da manyan shugabanni na ƙungiyoyin ta’addanci daban-daban.

Aikin ya kuma gano hanyoyin sadarwar kuɗaɗe da ake zargin suna tallafa wa ayyukan ta’addanci ta hanyar mu’amaloli ba bisa ƙa’ida ba da kuma damfara ta hanyar internet.

Hukumar ta ce an binciki mutane da kungiyoyi fiye da 15,000, inda aka gano kuɗaɗe da suka kai dalar Amurka miliyan 260 da ake zargin suna da alaƙa da ta’addanci, kuma an kwato sama da dalar Amurka 600,000.

Interpol ta bayyana cewa bincike ya kuma gano damfara ta hanyar internet, safarar kuɗi da amfani da kuɗaɗen internet wajen tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci.

Aikin ya samu haɗin gwiwar hukumar Interpol da tsarin haɗin gwiwar ‘yan sanda na Afirka (Afripol), kuma an gudanar da shi ƙarƙashin shirin ISPA da gwamnatin Jamus ta tallafa don yaƙi da laifukan ƙetare iyaka da ta’addanci a Afirka.

Hukumar ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike kan hanyoyin kuɗaɗen da ake zargin suna da alaƙa da ta’addanci domin gano sauran kadarori da hanyoyin da ake amfani da su.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here