Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta sanar da yin murabus ba tare da bata lokaci ba ga manyan jami’an ‘yan sandan da suka shafe sama da shekaru 35 suna aiki ko kuma sun haura shekaru 60 a duniya.
An cimma wannan matsaya ne a taron farko na musamman na hukumar na shekarar 2025, Wanda mataimakin Sufeto Janar Hashimu Argungu mai ritaya ya jagoranta.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka hada da mai shari’a Adamu Paul Galumje mai ritaya daga kotun koli, DIG Taiwo Lakanu mai ritaya, da sakataren hukumar Cif Onyemuchi Nnamani.
Sanarwar da mai magana da yawun Hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar ta bayyana cewa, wannan matakin ya yi daidai da dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 020908 (i & ii), wadda ta tanadi yin ritaya bayan ma’aikaci ya cika shekaru 35 yana aiki ko kuma ya cika shekaru 60 a duniya.
Karanta ƙarin labari: Rundunar yan sanda ta tabbatar da sake faɗuwar tankar man fetur a Jigawa
“A baya Hukumar ta amince a taronta na 24 a watan Satumba na 2017 cewa masu shiga rundunar su kasance da ranar nadin su daidai da ranar da za su shiga. Sai dai, bayan nazari, Hukumar ta gano cewa wannan shawarar ta saba wa ka’idojin hada-hadar hidima a cikin ma’aikatun gwamnati kuma ta saba ka’idojin ritaya,” in ji Ani.
Sanarwar ta kara da cewa, “An mika wa Sufeto Janar na ‘yan sanda hukuncin da hukumar ta yanke”.
Wannan ci gaban ya nuna wani muhimmin mataki na tabbatar da bin ka’idojin aikin gwamnati a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya.