Hotuna: Jamus ta bai wa Najeriya gumakanta 1,000 da aka sace a ƙarni na 19

321137206 1256930095039006 8663996558931332041 n
321137206 1256930095039006 8663996558931332041 n

Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock ta miƙa gumaka da sassaƙe-sassaƙe 20 ga gwamnatin Najeriya, waɗanda aka sace a ƙarni na 19.

Ministar ta miƙa su ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka yi a Abuja, babban birnin ƙasar.

An dawo da waɗannan gumaka na tagulla na Benin ne bayan da aka cimma wata yarjejeniya a farkon shekarar nan ta mayar da muhimman sassaƙe-sassaƙen fiye da 1,000 da mamallakansu na ainihi.

A watan Yuli ne, najeriya ta ce wannan ne karo na farko da wata ƙasar turai ta shiga irin wannan yarjejeniya.

Ms Baerbock ta ce hakan wani ƙoƙari ne na daƙushe “tarihin mulkin mallakar baƙaƙen fata” da aka yi.

Da take magana a wajen bikin a yau Talata, ta ƙara da cewa dama ce ta gyara wasu kura-kurai da aka yi a baya.

Da cikin abubuwan da aka mayar da su sun haɗa da wasu fitattun gumaka da sassaƙe-sassaƙe.

A baya-bayan nan ana samu ƙaruwa kiraye-kiraye kan ƙasashen Turai su mayar da kayayykin Afirka da suke maƙare a gidajen tarihinsu.

(BBC)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here