
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza masu kunna kida a wurin taruka da aka fi sani da DJ zuwa bukukuwan mata zalla a faɗin jihar.
Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka, yayin wani taro da wakilan ƙungiyar masu DJn a jihar ya bayyana matakin ya zama dole a ƙoƙarin da hukumar ke yi na daƙile cuɗanya tsakanin mata da maza a wuraren taruka.
Sheikh Daurawa ya ƙara da cewa daga yanzu mata kaɗai aka lamuncewa yin DJ a tarukan mata.
Karin labari: Alkaliyar Alkalai ta jihar Kano ta sauya kotun da za ta ci gaba da sauraron shari’ar Ganduje da wasu mutane 7
Shugaban na Hisba ya ce ”A matsayin jihar nan ta musulunci, ba za mu bari a dinga cuɗanya tsakanin mata da maza ba a wurin taro.
“Saboda hakan zai kawo ƙaruwa da kuma yaɗuwar baɗala.”
Ya ƙara da cewa a baya an yi wani taron da masu wuraren biki a jihar domin a wayar musu da kai kan dokokin da suka jiɓanci tafiyar da sana’artasu.
Karin labari: Naira ta kara daraja a kasuwa
Jagoran wakilan ƙungiyar masu DJ, Ibrahim Farawa wanda aka fi sani da DJ Farawa ya jinjina wa Hukumar kan gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta fitar don lura da al’amuran sana’ar tasu waɗanda suka haɗa da kiyaye lokutan sallah da kuma buƙatar hana cuɗanya tsakanin mata da maza yayin taruka.
DJ Farawa ya yi ƙira ga dukkan masu DJ da ke jihar da su bi dokokin da hukumar ta gabatar domin gujewa aikata laifi.
Karin labari: “Cin hanci da rashawar da mu ’yan siyasa ke yi idan mun sata tare da mutane mu ke rabawa” – Ndume
Sannan ya ƙara kira ga dukkan masu irin sana’ar da ke jihar da su yi rijista ƙarƙashin ƙungiyar domin amfana da tsare-tsaren da aka fitar.
Ya kuma gargaɗi waɗanda suka ƙi yin hakan da cewa ƙungiyar ba za ta kare duk wanda aka kama da laifin take dokokin Hisbah ba.