Hedikwatar tsaro ta musanta jita-jitar yunƙurin juyin mulki, ta tabbatar da biyayyarta ga Tinubu

DHQ spokesman Tukur Gusau 746x430

Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa an soke bukukuwan cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai saboda yunƙurin juyin mulki a matsayin labarin ƙarya da kuma makirci na ƙoƙarin tayar da hankalin jama’a.

Daraktan yada labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa rahoton ya haɗa da zarge-zargen da ba su da tushe dangane da binciken jami’an sojoji goma sha shida da ake yi a halin yanzu.

Gusau ya ce rundunar sojojin Najeriya ba ta taɓa yin magana ko nuni da wani yunƙurin juyin mulki ba, yana mai cewa labarin an kirkire shi ne don haifar da fargaba da rashin amincewa tsakanin ’yan ƙasa.

Ya bayyana cewa soke bikin ranar ’yancin kai an yi shi ne saboda tafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa wani muhimmin taron haɗin gwiwa na ƙasashen duniya a ƙetare, da kuma bai wa dakarun ƙasar damar ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci da kuma fatattakar ’yan ta’adda a sassan ƙasa.

Gusau ya ƙara da cewa binciken jami’an da ake yi a yanzu na cikin tsarin yau da kullum ne don tabbatar da ɗa’a da ƙwarewa a cikin rundunar sojoji, kuma sakamakon binciken zai kasance a fili idan an kammala.

Ya roƙi ’yan Najeriya da su yi watsi da wannan rahoto na ƙarya tare da ci gaba da goyon bayan jami’an tsaro wajen kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da cewa sojojin Najeriya suna nan daram cikin biyayya ga kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin tsaro, Bola Ahmed Tinubu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here