Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a wata Yuni

food market
food market

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a wata Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris ɗin 2023.

A wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar a yau Litinin, ta ce an samu ƙaruwar ne sakamakon canji da aka samu a farashin kayan abinci.

Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 22.25 wanda ya zarce kashi 20.60 da aka samu a watan Yunin 2022.

A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a ƙasar.

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here