Hauhawar farashin kaya a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 24.23 – NBS

Market women 1 750x430

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta ce, farashin kayayyaki ya samu hauhawa a watan Maris da ya gabata zuwa kashi 24.23 cikin 100 a sababbin alƙaluman da ta fitar.

Rahoton na NBS ta fitar a yau Talata ya nuna cewa an samu ƙarin hauhawar farashin da kashi 1.05 idan aka kwatanta da watan Fabrairu na 2024 daga 23.18 da aka samu a watan.

Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin a Najeriya tun bayan da hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta sauya ma’aunin da take amfani da shi wajen fitar da alƙaluman a farkon shekarar nan.

“Bugu da ƙari, alƙaluman saurin hauhawar farashin ya kai 3.90% a watan Maris na 2025 idan aka kwatanta da na Fabrairu, wanda yake 2.04%,” a cewar rahoton.

Karin karatu: Dokar ta ɓaci: Majalisar wakilai ta kaddamar da kwamitin wucin gadi mai mutum 21 da za su sa ido kan gwamnatin jihar Rivers

Ta ƙara da cewa bisa lissafin shekara-shekara, hauhawar kayan abinci kuma ta kai kashi 21.79 a watan Maris ɗin na 2025 idan aka kwatanta da Maris na 2024.

Ta ce abubuwan da suka fi jawo hauhawar farashin sun haɗa da abinci da kuma lemukan sha na kwalaba (kashi 9.28 cikin 100), da kuɗaɗen hayar gida da na wuraren sayar da abinci (kashi 2.99 cikin 100), da kuɗin sufuri ((kashi 2.47 cikin 100).

Sauran su ne kuɗin ruwa, wuta, iskar gas da sauran makamashi, ilimi, sai kuma harkokin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here