Hatsaniya ta ɓarke a taron Jam’iyyar APC a Gombe

Tinubu Shettima1 e1658330372980 680x365 c
Tinubu Shettima1 e1658330372980 680x365 c

An samu hatsaniya a taron da shugabannin jam’iyyar APC a yankin arewa Maso gabas da aka gudanar a Jihar Gombe.

Rikicin ya fara ne bayan da Kwamared Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da arewa maso gabas, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba kasa Bola Tinubu don ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar daga yankin sun halarci taron, ciki har da gwamnoni da ministoci da ‘yan majalisu.

Daga nan ne sai mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa Bukar Dalori, ya fito ya bayyana goyon baya ga Tinubu da kuma Shettima don su ci gaba da mulki a wani salo na kwantar da rikicin da ya taso.

Amma lamarin ya kara dagulewa ne bayan da shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi jawabi, inda ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu kadai, ba tare da ya ambaci Shettima ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here