Harin gidan gyaran halin Jos: Ƴan sanda sun kama fursunoni 8 da suka tsere

Jos Correctional Centre
Jos Correctional Centre

Rundunar ƴan sandan jihar Filato, ta ce ta kama 8 daga cikin fursunonin da suka tsere yayin harin da wasu ƴan bindiga suka kai gidan gyaran hali na Jos.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Ubah Ogaba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a birnin Jos.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya Nan ya rawaito cewa da yammacin jiya Lahadi ne wasu ƴan bindiga suka mamaye harabar gidan gyaran halin inda wasu daga cikin fursunonin da ke ciki suka tsere daga gidan.

Ogaba ya ce, daga cikin fursunonin 8 da suka tsere, 7 ƴan sanda sun sake kama su yayin da 1 ya miƙa kansa bisa raɗin kansa.

“A jiya, da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a cibiyar tsaro ta ‘yan sanda dake Jos.

“Nan da nan muka samu rahoton, kwamishinan ƴan sandan jihar Bartholomew Onyeka, ya ba da umarnin a killace cibiyar baki ɗaya.

Haka kuma ya ce, “Kwamishinan ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa sannan kuma fursunoni 7 da suka tsere ƴan sanda sun sake kama su kuma suna tsare”.

“Ɗaya daga cikinsu ya mika kansa ga ƴan sanda bisa raɗin kansa,” in ji Ogaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here