Hajjin 2026: Kano ta sanya Naira Miliyan 8.5m a matsayin kuɗin ajiya, daidai lokacin da NAHCON ta baiwa jihar kujeru 5,684

WhatsApp Image 2024 10 08 at 01.37.31 1 694x430

Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da cewa dole ne maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajji su biya kuɗin ajiya har Naira Miliyan 8,500,000 domin samun gurbin shiga aikin Hajji na shekarar 2026.

Babban Daraktan hukumar, Lamin Danbappa ne ya sanar da hakan a lokacin wani taro da mambobin hukumar da ma’aikatan gudanarwa da kuma jami’an cibiyar alhazai ta karamar hukumar.

A cewar wata sanarwa a ranar Laraba ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, Danbappa ya ce hukumar alhazai ta kasa ce ta tsayar da kudaden ajiya kuma za a karbe su nan take ta hanyar takardun banki da jami’an cibiyar alhazai na kananan hukumomi suka gabatar.

Shugaban ya kara da cewa an warewa jihar Kano jimillar kujeru 5,684 domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2026.

Labari mai alaƙa: 2026: NAHCON ta bude lasisin neman aikin jigilar Hajji don yin rijistar

Sanarwar ta kara da cewa za a fara tattara kudaden ajiya nan take kuma za a ci gaba da aiki har zuwa ranar rufewa a ranar 5 ga Oktoban 2025, lokacin da kuma za a bayyana kudin aikin Hajji na karshe.

Danbappa ya bukaci maniyyatan da suke son zuwa aikin Hajji da su rika biyan kudadensu a kan kari bisa ka’idojin da hukumomin Saudiyya suka fitar, ya kuma tunatar da su cewa rajista na bukatar fasfo na kasa da kasa da kuma hotuna masu girman fasfo guda takwas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here