Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) ta ja kunnan direbobi dangane da gudun wuci sa’a da suke a kan tituna musamman manyan titunan Najeriya.
Haka kuma hukumar ta bukaci Direbobin da su guji ketare mota wato Overtaking a titunan, wanda hakan ne zai sa a rage yawan samun asarar rayukan al’umma da ake samu sanadiyyar hatsari a manyan titunan na Najeriya.
Dr Samuel Ibitoye, shugaban hukumar ta FRSC a jihar ta Ondo ne ya bayyana hakan a garin Ore dake karamar hukumar Odigbon jihar ta Ondo, sakamkon wani hadari da aka samu a ranar Asabar 01/02/2025 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 28.
Karin karatu: Yan Daurin Aure 19 Sun Mutu A Hadarin Mota
Ibitoye ya Kuma bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa mutane 30 ne hadarin ya rutsa da su sakamakon tawo mugama da wasu motoci sukai a kan titin na Ore wanda yai sanadiyyar mutuwar mutanan 28.
Ya kuma shawarci direbobi da su rinka bin dokokin tuki yadda ya kamata musamman a manyan titunan kasar nan.
A cewar sa fasinjojima suna da hakkin a kaisu inda sukeso ba tare da wani abu ya samesu ba.