Haɗarin kwale-kwale a Neja ya hallaka mutane 29

154 feared dead in Kebbi boat mishap

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane ashirin da tara, yayin da wasu mutane biyu suka bace tare da ceto wasu 50 a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Borgu.

Rahotanni sun ce, hatsarin kwale-kwalen ya afku ne a Gausawa da ke yankin Malale na yankin tare da mutane 90.

Kazalika, jirgin ruwan ya taso ne daga Tugan Sule da ke unguwar Shagunu inda akasari mata da kananan yara ne.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa jirgin yayo lodi lokacin da suka taso daga Tunga Sule amma matsalar ta fara ne a Gausawa kuma ta kai ga kifewar jirgin nan take.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

Karanta: Gwamnatin Kano ta gargaɗi ƙungiyar tuntuɓa ACF kan sake kafa majalisar dattijai

Ya bayyana cewa an danganta lamarin ne da yawan lodi da kuma karo da kututturen bishiya a karkashin ruwa yayin da ya tabbatar da cewa fasinjojin ba su sanya rigar ceto ba duk da irin matakin da gwamnati ta dauka kan irin wannan aiki a jihar.

Arah ya ce an gano gawarwaki 29 tare da ceto mutane 50 da ransu yayin da wasu mutane 2 suka bace.

Darakta Janar din ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan ‘bincike da ceto’ domin yiwuwar samo mutanen da suka bata.NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here