Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare-gyaren da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aiwatar sun ceci akalla jihohi 27 a Najeriya daga durƙushewar tattalin arziƙi.
Mohammed Idris ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi a bikin yaye dalibai karo na 34 da bikin tunawa da kafuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna karo na 43, inda ya gabatar da lakca mai taken matasa da gina ƙasa a zamanin gyare-gyaren ƙasa.
A cewarsa, kafin ranar 29 ga Mayu 2023, kusan jihohi 27 a fadin ƙasar ba su da ikon biyan albashin ma’aikatansu, lamarin da ya nuna irin halin ƙunci da tattalin arziƙin jihohin ke ciki kafin fara aiwatar da gyare-gyaren.
Ya kara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya zagaya fadin ƙasar nan a lokacin kamfen da tsare-tsare na musamman na mayar da Najeriya ƙasa mafi girma, sannan bayan hawansa mulki ya kaddamar da sauye-sauyen da suka hana durƙushewar jihohin.
Ministan ya ce a halin yanzu jihohi na samun kudade har sau uku fiye da abin da suke samu a baya, lamarin da ya ba su damar biyan albashi, aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da kuma isar da ribar dimokuraɗiyya ga al’ummarsu.
Ya bayyana cewa waɗannan nasarori sun samu ne sakamakon gyare-gyaren Tinubu da kuma dabarun shugabanci masu inganci, inda ya jaddada cewa babu yadda za a gina ƙasa ba tare da ci gaba da aiwatar da gyare-gyare ba, domin gyare-gyare ne ke kare ƙasa daga fadawa matsalolin da sakaci ke haifarwa.
Ministan ya ce gyare-gyaren sun taimaka wajen gyara kura-kuran baya tare da ci gaba da tafiyar da tsarin gina ƙasa yadda ya kamata.
NAN













































