Gwamnonin Arewa da masu rike da sarautun gargajiya sun amince da kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a Najeriya, inda suka bukaci majalisar dokokin kasar da ta hanzarta aiwatar da tsarin doka.
Kudurin ya fito ne yayin wani taron hadin gwiwa na kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) da majalisun sarakunan jihohin Arewa 19 da aka yi a Kaduna a ranar Asabar 10 ga Mayu, 2025, inda suka mai da hankali kan tattauna rashin tsaro da ci gaban yankin.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban NSGF kuma Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ta bayyana cewa, “Kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga kafa rundunar ‘yan sandan jihar tare da yin kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta gaggauta daukar mataki kan samar da dokar da za ta fara aiki.”
Karin karatu: Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne – Kwankwaso
Ta kuma jaddada hadin kai ba tare da wata jam’iyya ba, da kuma bibiyar takwarorinsu domin tinkarar kalubalen yankin, inda ta yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa na magance matsalar tsaro da ababen more rayuwa a Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta kuduri aniyar karfafa ayyukan tsaro na cikin gida, da kafa dandali na hadin gwiwa tsakanin jihohi don sa ido kan iyakokin kasa, da hada kai da kungiyar gwamnonin Najeriya don bunkasa tallafi ga hukumomin tsaro na tarayya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Haka zalika, kungiyar ta yanke shawarar samar da hanyoyin shiga tsakanin jihohi cikin gaggawa don daidaita sa ido kan iyakokin, tare da bayyana tsarin bai daya na yaki da rashin tsaro.