Gwamnatin Zamfara ta mayar da Sarkin da ya naɗawa ƙasurgumin ɗan fashi sarauta

zamfara emir
zamfara emir

⁹Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya Muhammed Bello Matawalle, ya mayar wa Alh. Aliyu Garba Marafa sarautarsa ta sarkin Birnin Yandoto.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnan ya dakatar da sarkin saboda ya bai wa jagoran ‘yan bindiga Ado Aleiru sarautar sarkin Fulani a fadarsa.

Naɗin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar ne ta tabbatar da mayar da sarkin kan karagarsa.

Sanarwar ta ce an mayar da sarkin ne sakamakon buƙatar hakan daga kwamitin da gwamnati ta kafa domin bincike kan lamarin.

Tun da farko dai sarki ya ce ya bai wa Ado Aleiru sarautar ne sakamakon rawar da ya taka wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin masarautar da ‘yan bindigar da ke addabar ƙaramar hukumar Tsafe.

Sanarwar ta kara da cewa ”kwamitin bai samu wata hujja da ke nuna cewa sarkin na da wata mummunar manufa game da naɗin Ado Aleiru, ko haɗin baki tsakanin sarkin da ‘yan bindiga”.

“Sakamakon binciken kwamitin ya nuna cewa an naɗa Ado Aleiru ne a wani ɓangare na samar da zaman lafiya tsakanin tubabbun ‘yan bindiga da kuma garuruwan da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Tsafe da Gusau, wanda ya haɗa da garin Yandoto, don haka gwamnati ta mayar da sarkin ba tare da ɓata lokaci ba”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here