Gwamnatin tarayya za ta gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi kwanan nan a Yelwata, a Jihar Benue, a gaban kotu a ranar Litinin.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Ministan Shari’a kan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai, Kamarudeen Ogundele, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Mai shari’a Joyce Abdul-Malik na Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar 2 ga Fabrairu, 2026.
Ministan Shari’a na ƙasa kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a tabbatar da adalci a wannan lamari domin aika saƙo mai ƙarfi ga duk masu adawa da zaman lafiya da tsaron ƙasa ta kowace hanya.
Ya bayyana cewa an cimma wannan mataki ne bayan cikakken bincike mai zurfi da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati daban-daban.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa baki ɗaya, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
NAN













































