Gwamnatin tarayya ta sake buɗe shafin ɗaukar aikin Hukumomin kashe gobara da Civil Defence da sauran hukumomi

nscdc board

Hukumar Kula da rundunar Tsaro ta Civil Defence da ta gidan Gyaran hali da hukumar kasashe Gobara da Hukumar Kula da Shige da Fice ta (CDCFIB) ta ce, an sake buɗe shafin Internet don ɗaukar ma’aikata.

Hukumar ta sanar da dakatar da daukar ma’aikata a cikin hukumomin tsaron huɗu a makon da ya gabata bayan da shafin daukar ma’aikatan ya samu matsala.

Sanarwar na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da aka wallafa a  shafin X na hukuma ta (CDCFIB) a daren ranar Lahadi.

Ana shawartar masu neman aikin waɗanda suka yi nasarar fara cikewa da su, su koma shafin Internet su kammala a https://recruitment.cdcfib.gov.ng.

Hukumar ta ce, rufewar ya zama dole domin inganta tsarinta domin gudanar da dimbin aikace-aikace.

Haka kuma, hukumar ta bai wa ɗimbin ƴan Najeriya haƙuri bisa rufewar, ta na mai cewa ba wai ta yi shi ne da wata manufa ba illa inganta aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here