Gwamnatin tarayya ta kai karin kayan agaji ga al’ummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, biyo bayan wani mummunan harin da jiragen yakin sojoji ya kai a watan Disamban shekarar 2023.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, babban hafsan soji GOC shiyya ta daya kuma kwamandan sashe na 1, rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Mayirenso Saraso, ne ya bayyana hakan a madadin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.
NAN ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta gabatar da babura guda biyu da injinan janareta na Kamfanin Corolla da na’urar amsa kuwwa guda biyu da kayan sauti da da manyan fitulu masu karfin Watt 500 inda aka raba su ga mutanen da suka hada da Isuwa Haruna da Ridwan Yakubu da Isah Ahmed.
Saraso ya ce, matakin ya yi dai-dai da shawarwarin da wata tawagar gwamnatin tarayya da ta ziyarci al’ummar bayan afkuwar lamarin.
“Iftila’in na Tudun Biri ya faru ne a yayin wani farmakin da aka kai wa ‘yan bindiga da masu tsatsauran ra’ayi.
“Abin takaici, aikin ya haifar da asarar rayuka da barnata dukiya,” in ji GOC.
Ya sake mika sakon jajantawar rundunar Sojin Najeriya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.
Rundunar, in ji shi, ta himmatu wajen samar da taimako ga al’umma ta hanyar tallafi daban-daban da kuma hanyoyin farfado da su.
Shi ma da yake jawabi, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna, Dakta James Kanyip, ya bai wa al’ummar garin tabbacin cewa, gwamnatin jihar na ci gaba da bada goyon baya tare da tallafa wa mazauna yankin.













































