Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ‘yan kasuwar da ke da ɗabi’ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawan ƙasar nan ke cikin matsin rayuwa.
Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da ‘yan ƙasar ke ciki.
Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma.
Karanta wannan: Kano: Kotu ta buƙaci a yiwa Hafsat Chuchu gwajin ƙwaƙwalwa
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.
A cewar Idris, “Ma’aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau’in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa ‘yan ƙasar nan ba da jimawa ba”, in ji ministan.
Ya ƙara da cewa, “Gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa a faɗin ƙasar na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magana da su sun kuma amince za su fito da metric ton 60,000 don a sayarwa da ‘yan ƙasa.”
Karanta wannan: Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar canjin kudade
Ministan ya kuma gargaɗi masu ɓoye kayan abinci da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya.
Ya ci gaba da cewa, ”Ba abu ba ne na alkhairi ana cikin wannan matsi, kai kuma ka je ka ɓoye abinci don wata manufa taka ta daban, don haka gwamnati ke kira ga irin waɗannan ‘yan kasuwa da su fito da kayayyakin domin sauƙaƙawa ‘yan ƙasa” In ji ministan.
Yana mai cewa duk ɗan kasuwar da ya ki bin wannan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu.