Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙarin Naira dubu 32 kuɗin fansho ga masu ritaya

kano pensioners

Hukumar kula da tsare tsaren fansho (PTAD) ta bayyana cewa ta fara aiwatar da sabon ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikata da ke ƙarƙashin tsarin cin moriyar shirin adana kudade bayan ritaya wato Defined Benefit Scheme (DBS).

Wannan ƙarin ya haɗa da Naira 32,000, da kuma kashi 10.66 cikin 100 da 12.95 cikin 100 bisa tsarin da aka amince da shi, kuma zai fara aiki daga watan Satumbar 2025.

PTAD ta ce aiwatar da ƙarin ya biyo bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, wanda ya bayar da izinin ware kuɗin gaggawa domin taimakon masu ritaya.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan bayyana shirin a watan Agustan 2025.

Sabon tsarin yana daga cikin matakan gwamnati na inganta jin daɗin tsofaffin ma’aikata da suka yi wa ƙasa hidima tsawon shekaru.

Hukumar ta ƙara da cewa za a ci gaba da bin tsarin biyan kuɗaɗen yadda ya dace domin tabbatar da walwala da daidaituwar tsarin fansho a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa wannan mataki na ƙarin fansho zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da masu ritaya ke fuskanta a yanzu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here