Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ta ƙaddamar da sabon tsarin amfani da fasahar zamani domin inganta gaskiya, tsabtace lissafi da ingantaccen aiki a tsarin ilimin manyan makarantu na Najeriya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an sanya wa tsarin suna “Tsarin Gudanarwa da Gaskiya na Cibiyoyin Ilimi na Firamare da manyan Makarantu na Ƙasa”, wanda zai bai wa gwamnati damar bin diddigin yadda ake kashe kuɗaɗe, ci gaban aiki, da rarraba albarkatu a jami’o’i, kwalejoji, da makarantun kimiyya a ainihin lokacin.
Ministan ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ne ya ƙaddamar da wannan tsari a birnin Abuja a ranar Talata.
Ya bayyana cewa wannan mataki yana cikin tsarin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da gaskiya da kyakkyawan tsarin tafiyar da gwamnati a dukkan hukumomin gwamnati.
Alausa ya ce an ƙirƙiri FTIGTP ne domin bai wa al’umma damar ganin yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati a manyan makarantu, tare da tabbatar da cewa rarraba albarkatu yana ka. gaskiya da ƙa’ida.
Ya ƙara da cewa tsarin zai tattara bayanan dukkan cibiyoyin ilimi a wuri guda, domin sauƙaƙa bibiyar ayyuka da tabbatar da amfanar kuɗaɗen gwamnati.
Ya bayyana cewa tsarin zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya ta fuskar kuɗi, hana almundahana, da ƙarfafa amincewar jama’a ga shugabancin cibiyoyin ilimi. Haka kuma, an tsara shi domin bai wa hukumomi damar nazari da yin kwatancen ci gaban kowane jami’a ko makaranta.
Ministan ya ƙara jan hankalin jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi da su bi umarnin bayar da bayanai cikin lokaci, domin rahotannin kuɗaɗe za su zama wani ɓangare na tantancewa daga abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen waje.
A cewar sa, nan gaba kudade da tallafi za su dogara ne da yadda kowace cibiya ke aiwatar da gaskiya da tsabtace lissafi.
A nata jawabin, karamar ministar ilimi ta yaba da wannan mataki, tana mai cewa yana nuna sabon salo na tafiyar da harkokin ilimi ta hanyar amfani da bayanai da fasahar zamani.
Ta kuma bukaci dukkan cibiyoyin ilimi su yi amfani da tsarin yadda ya kamata tare da sabunta bayanai akai-akai domin dorewar tsarin.











































