Gwamnatin tarayya ta fara aikin gyara ƙarancin albashin watan Janairu – JPSNC

Civil Servants

Hukumar tattaunawa ta ma’aikatan gwamnatin tarayya (JPSNC) ta tabbatar wa ma’aikatan tarayya cewa gwamnati na magance sabanin da aka samu a cikin albashin watan Janairu, wanda aka ce ya yi kasa fiye da watannin baya.

Benjamin Anthony, shugaban majalisar na kasa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a Abuja.

Anthony yana maida martani ne kan damuwar da wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya suka nuna game da karancin albashin watan Janairu.

Ya bayyana cewa an samu matsalar ne bisa kuskure na tsari amfani da (IPPIS).

Karin labari: Kungiyar Kwadago ta sanar da ranar da za ta fara yajin aiki kan sabon mafi karancin albashi

“Mun sami korafe-korafe, ko da yake ba a rubuce ba, daga ma’aikata game da rage albashin su na watan Janairu idan aka kwatanta da abin da suka samu a watan Oktoba zuwa Disambar 2024.

Anthony ya bukaci ma’aikatan da abin ya shafa da su bayar da rahoto a hukumance ta hanyar kungiyoyinsu na ma’aikata don ba da taimako.

Anthony ya umurci ma’aikatan da abin ya shafa da su duba tsarin albashinsu don tantance abin da suke samu kafin su kai ga fuskantar matsalar.

Ya ce wani bangare na matsalolin na da nasaba da irin alawus na musamman da majalisar ta tattauna da gwamnati har ma ta amince ta ci gaba da biya, amma da alama tsarin IPPIS ya yi watsi da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here