Gwamnatin tarayya ta ce ta daina yanke kuɗaɗen jihohi na Paris Club

1684920495119
1684920495119

Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya (NGF) ta ce gwamnatin tarayyar ta amince ta dakatar da yankar kudade daga asusun jihohi a kan bashin London da Paris Club.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa takwarorinsa bayani a ganawar da suka yi jiya Talata a Abuja.

Haka kuma ya ce ministar kudi ta yi alkawarin tabbatar da ganin an mayar wa da jihohin kudin da aka yanke a baya.

Batun yankar kudin na Paris Club ya kasance babban abin takaddama tsakanin gwamnatin tarayyar da da gwamnatin jihohi a baya-bayan nan.

Takardar bayan taron ta kuma nuna cewa an samu sabon shugabanci a kungiyar inda mambobin suka amince ta hanyar sasanto gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya zama sabon shugaba, yayin da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya zama mataimaki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here